Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Filibbiyawa 4:14kusan 64 M.

    Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.

  2. Filibbiyawa 4:15kusan 64 M.

    Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai;

  3. Filibbiyawa 4:16kusan 64 M.

    gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata.

  4. Filibbiyawa 4:17kusan 64 M.

    Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku.

  5. Filibbiyawa 4:18kusan 64 M.

    An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.

  6. Filibbiyawa 4:19kusan 64 M.

    Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  7. Filibbiyawa 4:20kusan 64 M.

    Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.

  8. Filibbiyawa 4:21kusan 64 M.

    Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu. ’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku.

  9. Filibbiyawa 4:22kusan 64 M.

    Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.

  10. Filibbiyawa 4:23kusan 64 M.

    Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.

  11. Kolossiyawa 1:1kusan 64 M.

    Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,

  12. Kolossiyawa 1:2kusan 64 M.

    Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi. Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku.

  13. Kolossiyawa 1:3kusan 64 M.

    Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku.

  14. Kolossiyawa 1:4kusan 64 M.

    Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka.

  15. Kolossiyawa 1:5kusan 64 M.

    Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar

  16. Kolossiyawa 1:6kusan 64 M.

    da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta.

  17. Kolossiyawa 1:7kusan 64 M.

    Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu,

  18. Kolossiyawa 1:8kusan 64 M.

    wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.

  19. Kolossiyawa 1:9kusan 64 M.

    Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.

  20. Kolossiyawa 1:10kusan 64 M.

    Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah.

  21. Kolossiyawa 1:11kusan 64 M.

    Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki

  22. Kolossiyawa 1:12kusan 64 M.

    kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske.

  23. Kolossiyawa 1:13kusan 64 M.

    Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna,

  24. Kolossiyawa 1:14kusan 64 M.

    wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

  25. Kolossiyawa 1:15kusan 64 M.

    Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta.