Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Kolossiyawa 1:16kusan 64 M.

    Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne.

  2. Kolossiyawa 1:17kusan 64 M.

    Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.

  3. Kolossiyawa 1:18kusan 64 M.

    Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici.

  4. Kolossiyawa 1:19kusan 64 M.

    Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi,

  5. Kolossiyawa 1:20kusan 64 M.

    ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.

  6. Kolossiyawa 1:21kusan 64 M.

    A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku.

  7. Kolossiyawa 1:22kusan 64 M.

    Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.

  8. Kolossiyawa 1:23kusan 64 M.

    Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.

  9. Kolossiyawa 1:24kusan 64 M.

    Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.

  10. Kolossiyawa 1:25kusan 64 M.

    Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai.

  11. Kolossiyawa 1:26kusan 64 M.

    Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka.

  12. Kolossiyawa 1:27kusan 64 M.

    Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.

  13. Kolossiyawa 1:28kusan 64 M.

    Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi.

  14. Kolossiyawa 1:29kusan 64 M.

    Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.

  15. Kolossiyawa 2:1kusan 64 M.

    Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba.

  16. Kolossiyawa 2:2kusan 64 M.

    Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa,

  17. Kolossiyawa 2:3kusan 64 M.

    a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani.

  18. Kolossiyawa 2:4kusan 64 M.

    Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yă ruɗe ku da daɗin baki.

  19. Kolossiyawa 2:5kusan 64 M.

    Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.

  20. Kolossiyawa 2:6kusan 64 M.

    To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,

  21. Kolossiyawa 2:7kusan 64 M.

    ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.

  22. Kolossiyawa 2:8kusan 64 M.

    Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.

  23. Kolossiyawa 2:9kusan 64 M.

    Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata,

  24. Kolossiyawa 2:10kusan 64 M.

    an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.

  25. Kolossiyawa 2:11kusan 64 M.

    A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.