Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Kolossiyawa 3:14kusan 64 M.

    Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

  2. Kolossiyawa 3:15kusan 64 M.

    Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

  3. Kolossiyawa 3:16kusan 64 M.

    Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

  4. Kolossiyawa 3:17kusan 64 M.

    Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

  5. Kolossiyawa 3:18kusan 64 M.

    Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

  6. Kolossiyawa 3:19kusan 64 M.

    Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

  7. Kolossiyawa 3:20kusan 64 M.

    ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

  8. Kolossiyawa 3:21kusan 64 M.

    Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

  9. Kolossiyawa 3:22kusan 64 M.

    Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji.

  10. Kolossiyawa 3:23kusan 64 M.

    Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.

  11. Kolossiyawa 3:24kusan 64 M.

    Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.

  12. Kolossiyawa 3:25kusan 64 M.

    Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.

  13. Kolossiyawa 4:1kusan 64 M.

    Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.

  14. Kolossiyawa 4:2kusan 64 M.

    Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.

  15. Kolossiyawa 4:3kusan 64 M.

    Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi.

  16. Kolossiyawa 4:4kusan 64 M.

    Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata.

  17. Kolossiyawa 4:5kusan 64 M.

    Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi.

  18. Kolossiyawa 4:6kusan 64 M.

    Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

  19. Kolossiyawa 4:7kusan 64 M.

    Tikikus shi ne ƙaunataccen ɗan’uwan nan, wanda ya yi aiki da aminci a hidimar Ubangiji tare da mu, zai kuwa faɗa muku dukan labari game da ni.

  20. Kolossiyawa 4:8kusan 64 M.

    Ina aikansa shi a gare ku musamman domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.

  21. Kolossiyawa 4:9kusan 64 M.

    Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku. Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan.

  22. Kolossiyawa 4:10kusan 64 M.

    Aristarkus yana a kurkuku tare da ni. Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas. (Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.)

  23. Kolossiyawa 4:11kusan 64 M.

    Yesu, wannan da muke kira Yustus, shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni.

  24. Kolossiyawa 4:12kusan 64 M.

    Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana addu’a dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke.

  25. Kolossiyawa 4:13kusan 64 M.

    Na tabbatar muku, cewa yana aiki ƙwarai dominku da kuma domin waɗanda suke a Lawodiseya da Hiyerafolis.