Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa,

  2. muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.

  3. Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.

  4. Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,

  5. waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane

  6. suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.

  7. Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku.

  8. Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu.

  9. Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne?

  10. Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.

  11. Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai.

  12. Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku,

  13. don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan.

  14. Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani.

  15. Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.

  16. Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku.

  17. Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku.

  18. Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji.

  19. Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku?

  20. Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.

  21. Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku.

  22. Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku.

  23. Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.

  24. A ƙarshe, ’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau.

  25. Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.