Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.

  2. Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

  3. To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.

  4. Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.

  5. Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.

  6. Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.

  7. Ku riƙa farin ciki kullum;

  8. ku ci gaba da yin addu’a;

  9. ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

  10. Kada ku danne aikin Ruhu.

  11. Kada ku rena annabci,

  12. amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,

  13. ku ƙi kowace mugunta.

  14. Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  15. Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.

  16. ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.

  17. Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki.

  18. Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa.

  19. Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.

  20. Bulus, da Sila, da Timoti, Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi.

  21. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

  22. Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa.

  23. Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.

  24. Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala.

  25. Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala