circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Tessalonikawa 4:3kusan 54 M.
Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci;
- 1 Tessalonikawa 4:4kusan 54 M.
don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma,
- 1 Tessalonikawa 4:5kusan 54 M.
ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;
- 1 Tessalonikawa 4:6kusan 54 M.
cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi.
- 1 Tessalonikawa 4:7kusan 54 M.
Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.
- 1 Tessalonikawa 4:8kusan 54 M.
Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
- 1 Tessalonikawa 4:9kusan 54 M.
Yanzu kuwa game da ƙaunar ’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna.
- 1 Tessalonikawa 4:10kusan 54 M.
Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan ’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku yi haka sau da sau.
- 1 Tessalonikawa 4:11kusan 54 M.
Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku,
- 1 Tessalonikawa 4:12kusan 54 M.
don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.
- 1 Tessalonikawa 4:13kusan 54 M.
’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege.
- 1 Tessalonikawa 4:14kusan 54 M.
Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.
- 1 Tessalonikawa 4:15kusan 54 M.
Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba.
- 1 Tessalonikawa 4:16kusan 54 M.
Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko.
- 1 Tessalonikawa 4:17kusan 54 M.
Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.
- 1 Tessalonikawa 4:18kusan 54 M.
Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
- 1 Tessalonikawa 5:1kusan 54 M.
To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,
- 1 Tessalonikawa 5:2kusan 54 M.
gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.
- 1 Tessalonikawa 5:3kusan 54 M.
Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
- 1 Tessalonikawa 5:4kusan 54 M.
Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
- 1 Tessalonikawa 5:5kusan 54 M.
Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.
- 1 Tessalonikawa 5:6kusan 54 M.
Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
- 1 Tessalonikawa 5:7kusan 54 M.
Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
- 1 Tessalonikawa 5:8kusan 54 M.
Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
- 1 Tessalonikawa 5:9kusan 54 M.
Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.