circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Kolossiyawa 2:12kusan 64 M.
Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.
- Kolossiyawa 2:13kusan 64 M.
Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu.
- Kolossiyawa 2:14kusan 64 M.
Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye.
- Kolossiyawa 2:15kusan 64 M.
Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.
- Kolossiyawa 2:16kusan 64 M.
Saboda haka kada ku bar wani yă shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci.
- Kolossiyawa 2:17kusan 64 M.
Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu.
- Kolossiyawa 2:18kusan 64 M.
Kada ku yarda wani yă ɓata ku, cewa shi wani abu ne don yă ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yă kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka.
- Kolossiyawa 2:19kusan 64 M.
Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yă yi girma.
- Kolossiyawa 2:20kusan 64 M.
Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa,
- Kolossiyawa 2:21kusan 64 M.
“Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”?
- Kolossiyawa 2:22kusan 64 M.
Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane.
- Kolossiyawa 2:23kusan 64 M.
Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.
- Kolossiyawa 3:1kusan 64 M.
Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah.
- Kolossiyawa 3:2kusan 64 M.
Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.
- Kolossiyawa 3:3kusan 64 M.
Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah.
- Kolossiyawa 3:4kusan 64 M.
Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.
- Kolossiyawa 3:5kusan 64 M.
Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.
- Kolossiyawa 3:6kusan 64 M.
Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan.
- Kolossiyawa 3:7kusan 64 M.
Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali.
- Kolossiyawa 3:8kusan 64 M.
Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku.
- Kolossiyawa 3:9kusan 64 M.
Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa
- Kolossiyawa 3:10kusan 64 M.
kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.
- Kolossiyawa 3:11kusan 64 M.
A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.
- Kolossiyawa 3:12kusan 64 M.
Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa.
- Kolossiyawa 3:13kusan 64 M.
Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.