Tsallake zuwa abun ciki

circa 1406–1380 BC

Conquest of Canaan

Joshua leads Israel across the Jordan into the promised land, defeating the Canaanite kingdoms one by one.

658 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Yoshuwa 2:8kusan 1451 K.H.

    Kafin ’yan leƙen asirin su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin

  2. Yoshuwa 2:9kusan 1451 K.H.

    ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya riga ya ba ku ƙasan nan, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.

  3. Yoshuwa 2:10kusan 1451 K.H.

    Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai.

  4. Yoshuwa 2:11kusan 1451 K.H.

    Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa.

  5. Yoshuwa 2:12kusan 1451 K.H.

    Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa

  6. Yoshuwa 2:13kusan 1451 K.H.

    za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da ’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.”

  7. Yoshuwa 2:14kusan 1451 K.H.

    Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”

  8. Yoshuwa 2:15kusan 1451 K.H.

    Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.

  9. Yoshuwa 2:16kusan 1451 K.H.

    Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”

  10. Yoshuwa 2:17kusan 1451 K.H.

    Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba

  11. Yoshuwa 2:18kusan 1451 K.H.

    sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.

  12. Yoshuwa 2:19kusan 1451 K.H.

    In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.

  13. Yoshuwa 2:20kusan 1451 K.H.

    In kika tone mana asiri, za mu karya alkawarin da kika sa muka yi.”

  14. Yoshuwa 2:21kusan 1451 K.H.

    Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.” Sai ta sallame su suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan ƙyalle a tagar.

  15. Yoshuwa 2:22kusan 1451 K.H.

    Sai suka tafi, suka shiga cikin tuddai, suka yi zamansu a can kwana uku har masu nemansu suka koma, gama masu nemansu suka yi ta nema ko’ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba.

  16. Yoshuwa 2:23kusan 1451 K.H.

    Sa’an nan mutanen nan biyu, ’yan leƙen asiri suka sauka daga tuddai suka haye kogi zuwa wurin Yoshuwa ɗan Nun, suka gaya masa duk abin da ya faru da su.

  17. Yoshuwa 2:24kusan 1451 K.H.

    Suka ce wa Yoshuwa, “Ba shakka Ubangiji ya ba mu ƙasan nan duka, tana hannunmu, mutane can duk sun narke da tsoro saboda mu.”

  18. Yoshuwa 3:1kusan 1451 K.H.

    Kashegari Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Shittim suka nufi Urdun inda suka sauka kafin su haye.

  19. Yoshuwa 3:2kusan 1451 K.H.

    Bayan kwana uku sai shugabannin suka zazzaga sansani, suna

  20. Yoshuwa 3:3kusan 1451 K.H.

    ba da umarni ga mutane, suna cewa, “Lokacin da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, da firistoci waɗanda su ne Lawiyawa, suna ɗauke da shi, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi.

  21. Yoshuwa 3:4kusan 1451 K.H.

    A ta haka za ku san inda za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai ku ɗan ba da rata wajen yadi ɗari tara tsakaninku da akwatin alkawari, kada ku kusace shi.”

  22. Yoshuwa 3:5kusan 1451 K.H.

    Yoshuwa ya ce wa mutane, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai yi abubuwan al’ajabi a cikinku.”

  23. Yoshuwa 3:6kusan 1451 K.H.

    Yoshuwa ya ce wa firistoci, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku sha gaba.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban sauran jama’a.

  24. Yoshuwa 3:7kusan 1451 K.H.

    Ubangiji kuwa ya ce wa Yoshuwa, “Yau, zan fara ɗaukaka ka a gaban Isra’ilawa duka don su sani cewa ina tare da kai kamar yadda na kasance tare da Musa.

  25. Yoshuwa 3:8kusan 1451 K.H.

    Ka ce wa firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, ‘Sa’ad da kuka kai bakin Urdun, ku shiga cikin ruwan ku tsaya.’ ”