Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar.

  2. “Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”

  3. Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.

  4. Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.”

  5. “Ka faɗa wa Isra’ilawa, su juya su kafa sansani a Fi Hahirot, a tsakanin Migdol da teku. Za su kafa sansanin kai tsaye kusa da teku, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.

  6. Fir’auna zai yi tsammani, ‘Aha, Isra’ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta yimƙe su.’

  7. Sa’ad da aka faɗa wa Fir’auna cewa Isra’ilawa sun gudu, sai Fir’auna da bayinsa suka canja ra’ayinsu game da su, suka ce, “Me muka yi? Mun bar Isra’ilawa suka tafi, mun kuwa rasa hidimarsu!”

  8. Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna sarkin Masar, domin yă bi Isra’ilawa waɗanda suke tafiya ba tsoro.

  9. Da Fir’auna ya yi kusa, Isra’ilawa suka ɗaga idanu sai suka hange Masarawa daga nesa suna tā da ƙura suna zuwa. Sai suka tsorata ƙwarai, suka kuwa yi kuka ga Ubangiji.

  10. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Don me kake mini kuka? Ka faɗa wa Isra’ilawa su ci gaba da tafiya.

  11. Ka ɗaga sandanka, ka miƙa shi bisa teku don ruwa yă rabu domin Isra’ilawa su wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa.

  12. Sai mala’ikan Allah wanda yake tafiya a gaban sojojin Isra’ila, ya janye, ya koma bayansu. Al’amudin girgije shi ma ya koma, ya tsaya a bayansu,

  13. ya dawo tsakanin sojojin Masar da na Isra’ila. Duk dare, girgijen ya jawo duhu ga gefe ɗaya, haske kuma ga ɗaya gefen; saboda haka ba wanda ya kusaci wani duk dare.

  14. sai Isra’ilawa suka wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa, ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.

  15. Ya sa ƙafafun keken yaƙinsu suka fita don su kāsa tuƙi. Sai Masarawa suka ce, “Bari mu gudu daga Isra’ilawa gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masar.”

  16. Amma Isra’ilawa suka wuce cikin teku a busasshiyar ƙasa, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu.

  17. A rana nan Ubangiji ya cece Isra’ila daga hannuwan Masarawa, Isra’ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin teku.

  18. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga iko mai girma da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa, sai mutanen suka ji tsoron Ubangiji, suka amince da shi, da kuma bawansa Musa.

  19. Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan rera waƙa ga Ubangiji gama an ɗaukaka shi ƙwarai. Doki da mahayinsa ya jefa su cikin teku.

  20. Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.

  21. Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.

  22. Dukan taron Isra’ila suka tashi daga Elim suka zo hamadar Sin, wadda take tsakanin Elim da Sinai, a rana ta goma sha biyar ga wata biyu, bayan sun fito daga Masar.

  23. A hamadan, dukan taro suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna.

  24. Isra’ilawa suka ce musu, “Da ma a hannun Ubangiji ne muka mutu a Masar, inda muka zauna kewaye da tukwanen nama, muna cin duk abincin da muke so, amma kun kawo mu cikin wannan hamada don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”

  25. Saboda haka Musa da Haruna suka ce wa dukan Isra’ila, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fitar da ku daga Masar.