Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka faɗa wa dukan taron Isra’ila, ‘Ku zo gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninku.’ ”

  2. Yayinda Haruna yake magana da dukan taron Isra’ila, sai suka duba wajen hamada, sai ga ɗaukakar Ubangiji tana bayyana a girgije.

  3. “Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  4. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, “Mene ne wannan?” Gama ba su san ko mene ne ba. Musa ya ce musu, “Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci.

  5. Isra’ilawa suka yi kamar yadda aka faɗa musu, waɗansu suka tattara da yawa, waɗansu kuma kaɗan.

  6. Mutanen Isra’ila suka kira burodin Manna. Manna yana nan fari kamar farin riɗi, ɗanɗanonsa kuma yana kama da masa da aka yi da zuma.

  7. Isra’ilawa suka yi shekaru arba’in suna cin Manna, har sai da suka shiga cikin ƙasar da take da mutane, suka ci Manna har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana.

  8. Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha.

  9. Ubangiji amsa wa Musa, “Ka ɗauki sandan da ka bugi ruwan Nilu da shi. Ka kira waɗansu shugabannin Isra’ila, ku wuce a gaban jama’ar.

  10. Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila.

  11. Sai suka ba wa wurin suna, Massa da Meriba, saboda Isra’ilawa sun yi jayayya, suka kuma gwada Ubangiji cewa, “Ubangiji yana tsakaninmu ko babu?”

  12. Amalekawa suka zo, suka yaƙi Isra’ilawa a Refidim.

  13. Muddin hannun Musa yana a miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara.

  14. Ana nan sai Yetro firist na Midiyan, kuma surukin Musa, ya ji duk abin da Allah ya yi wa Musa da mutanensa Isra’ila, da kuma yadda Ubangiji ya fitar da Isra’ila daga Masar.

  15. Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa.

  16. Sa’an nan Yetro surukin Musa, ya kawo hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu wa Allah, Haruna ya zo tare da dukan dattawan Isra’ila, suka ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.

  17. Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.

  18. A rana ta farko a cikin watan uku bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, a wannan rana, suka iso Hamadar Sinai.

  19. Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen.

  20. Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila.

  21. za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”

  22. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa wannan. ‘Kun gani da kanku cewa na yi magana da ku daga sama.

  23. Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku hauro zuwa wurina, kai da Haruna, Nadab da Abihu, da kuma dattawa saba’in a cikin Isra’ila. Za ku yi sujada da ɗan nisa,

  24. Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila.

  25. Sai ya aiki samarin Isra’ilawa, suka miƙa hadaya ta ƙonawa, suka kuma miƙa ƙananan bijimai don hadaya ta salama ga Ubangiji.