Skip to content

Bilhah

10 ayoyi · 3 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Bilhah

  1. Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa ’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta.

  2. Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini ’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.”

  3. Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita,

  4. ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa.

  5. Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu.

  6. Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari. Yaƙub ya haifi ’ya’ya maza goma sha biyu.

  7. ’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne, Dan da Naftali.

  8. Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.

  9. Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne.

  10. ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yaziyel, Guni, Yezer da Shallum, su zuriyar Bilha ne.