Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  2. ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

  3. Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  4. Bulus, da Sila, da Timoti, Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi.

  5. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

  6. Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa.

  7. Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.

  8. Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala.

  9. Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala

  10. Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba.

  11. Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza.

  12. Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.

  13. Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.

  14. Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya

  15. Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya.

  16. Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,

  17. Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.

  18. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,

  19. Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.

  20. da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.

  21. Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.

  22. Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu,

  23. Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu,

  24. (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)

  25. in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jama’ar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya.