Tsallake zuwa abun ciki

David

968 ayoyi · 40 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci David

Tace bisa littafi
  1. Sai mutumin Allah ya tā da murya a kan bagade bisa ga umarnin Ubangiji ya ce, “Ya bagade, bagade! Ubangiji ya ce, ‘Za a haifi ɗa mai suna Yosiya wa gidan Dawuda. A kanka zai miƙa firistoci na masujadai kan tuddai masu miƙa hadayu a nan, za a kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kanka.’ ”

  2. Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba da shi gare ka, amma ba ka zama kamar bawana Dawuda wanda ya kiyaye umarnaina ya kuma bi ni da dukan zuciyarsa, yana yin abin da yake daidai kaɗai a idanuna ba.

  3. Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  4. Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba.

  5. Duk da haka, saboda Dawuda Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima ta wurin ta da wani da ya gāje shi, ta wurinsa kuma Urushalima ta yi ƙarfi.

  6. Gama Dawuda ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, bai kuma fasa kiyaye wani daga umarnan Ubangiji ba dukan kwanakinsa, sai dai a batun Uriya mutumin Hitti.

  7. Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.

  8. Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.

  9. Sai Asa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin kakansa Dawuda. Sai Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  10. Yehoshafat kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin Dawuda kakansa. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi.

  11. Duk da haka, saboda bawansa Dawuda, Ubangiji bai ragargaza Yahuda ba. Ya riga ya yi alkawari zai bar wa Dawuda magāji har abada.

  12. Yoram ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda. Sai Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  13. Barorinsa suka ɗauke shi cikin keken yaƙi zuwa Urushalima suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

  14. Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.

  15. Hafsoshin da suka kashe shi kuwa su ne Yozabad ɗan Shimeyat da Yehozabad ɗan Shomer. Ya mutu, aka kuma binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda. Sai Amaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  16. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, sai dai ba kamar kakansa Dawuda ba. A kome dai ya bi gurbin mahaifinsa Yowash.

  17. Aka ɗauko shi a kan doki aka kawo shi Urushalima, aka kuwa binne shi tare da kakanninsa, a Birnin Dawuda.

  18. Azariya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi kusa da su a Birnin Dawuda. Yotam ɗansa, kuma ya gāje shi.

  19. Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda, birnin mahaifinsa. Ahaz ɗansa kuma ya gāje shi.

  20. Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba.

  21. Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi da su a Birnin Dawuda. Hezekiya ɗansa kuma ya gāje shi.

  22. Sa’ad da ya ware Isra’ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat sarki a kansu. Yerobowam ya rinjayi Isra’ila daga ƙin Ubangiji, ya sa suka aikata babban zunubi.

  23. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda kakansa Dawuda ya yi.

  24. Zan kāre birnin nan in cece ta, saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”

  25. “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji.