Tsallake zuwa abun ciki

David

968 ayoyi · 40 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci David

Tace bisa littafi
  1. Ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya kusa da Amasa ya ce, “Duk mai son Yowab, kuma duk mai son Dawuda, yă bi Yowab!”

  2. Ba haka ba ne batun. Wani mai suna Sheba ɗan Bikri ne, daga ƙasar tudun Efraim, ya tayar wa sarki, yana gāba da Dawuda. Ki ba mu wannan mutum, zan kuwa janye daga birnin.” Matar ta ce wa Yowab, “Za a jefa maka kansa daga katanga.”

  3. Ira mutumin Yayir kuwa shi ne firist na Dawuda.

  4. Lokacin da Dawuda yake mulki, an yi yunwa shekara uku a jere; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce, “Saboda Shawulu ne da alhakin jinin gidansa; domin ya kashe Gibeyonawa.”

  5. Dawuda ya ce wa Gibeyonawa, “Me zan yi muku? Yaya zan yi kafara domin ku sa wa masu gādon Ubangiji albarka?”

  6. Sarki ya ware Mefiboshet ɗan Yonatan jikan Shawulu, saboda rantsuwar da take tsakanin Dawuda da Yonatan, ɗan Shawulu a gaban Ubangiji.

  7. Da aka gaya wa Dawuda abin da Rizfa ’yar Aiya ƙwarƙwaran Shawulu ta yi,

  8. sai ya je ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga mutanen Yabesh Gileyad (Gama mutanen sun saci gawawwakin Shawulu da Yonatan daga inda Filistiyawa suka kakkafa su a kan itace a filin Bet-Shan, bayan da Filistiyawa suka kashe su a Gilbowa.)

  9. Har yanzu yaƙi ya sāke ɓarke tsakanin Filistiyawa da Isra’ila. Sai Dawuda ya gangara tare da mutanensa don su yaƙi Filistiyawa, gajiya ta kama shi.

  10. Ishbi-Benob kuwa, wani daga zuriyar Rafa, wanda nauyin kan māshinsa na tagulla ya yi shekel ɗari uku, wanda yake kuma da sabon māshi, ya ce zai kashe Dawuda.

  11. Amma Abishai ɗan Zeruhiya ya kawo wa Dawuda gudummawa; ya bugi Bafilistin, ya kashe shi. Sa’an nan mutanen Dawuda suka rantse masa suka ce, “Ba za ka ƙara fita tare da mu wurin yaƙi ba, don kada fitilar Isra’ila tă mutu.”

  12. Da ya yi wa Isra’ila reni, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwa Dawuda, ya kashe shi.

  13. Waɗannan huɗu zuriyar Rafa ne a Gat, suka kuwa mutu ta hannu Dawuda da mutanensa.

  14. Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.

  15. “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”

  16. Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe. “Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai, abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama. Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki, wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila.

  17. Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.

  18. Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,

  19. A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.

  20. Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.

  21. Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”

  22. Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.

  23. Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

  24. Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.”

  25. Bayan Dawuda ya ƙidaya mayaƙan, lamirinsa ya kāshe shi, sai ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka ka gafarta wa bawanka. Na yi wauta ƙwarai.”