Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Watchfulness

167 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’

  2. “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’

  3. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.

  4. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”

  5. Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba?

  6. Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

  7. Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.

  8. “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.

  9. Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.

  10. Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

  11. “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.

  12. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

  13. “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’tsaye indabai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.

  14. Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu.

  15. Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa.

  16. Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!

  17. Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi.

  18. Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.

  19. “Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin.

  20. A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata.

  21. Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.

  22. Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.

  23. “Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai.

  24. Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba.

  25. Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro.