Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Stars

57 ayoyi · 40 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

  2. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  3. Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

  4. Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.

  5. Ku ɗaga idanunku ku duba sammai. Wane ne ya halicce dukan waɗannan? Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya, yana kiransu, kowanne da sunansa. Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma, babu ko ɗayansu da ya ɓace.

  6. Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! Bari masananki na taurari su zo gaba, waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.

  7. Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa.

  8. Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ”

  9. Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya kafa rana don tă yi haske a yini shi da ya sa wata da taurari su yi haske da dare, shi da yake dama teku don raƙuman ruwansa su yi ruri Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

  10. “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,” in ji Ubangiji, “to, sai zuriyar Isra’ila ta daina zama al’umma a gabana.”

  11. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci duniya, Ubangiji wanda ya siffanta ta ya kuma kafa ta, Ubangiji ne sunansa.

  12. Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’ ”

  13. Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu; zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba.

  14. Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su.

  15. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

  16. A gabansu duniya takan girgiza, sararin sama kuma yakan jijjigu, rana da wata su yi duhu, taurari kuma ba sa ba da haske.

  17. Za a duhunta rana da wata, taurari kuma ba za su ba da haske ba.

  18. (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, wanda ya mai da duhu ya zama haske ya kuma baƙanta rana ta zama dare, yakan kwashe ruwan teku ya zubar a ƙasa, Ubangiji ne sunansa,

  19. Kun ɗaga masujadar sarkinku, siffofin gumakanku, tauraron allahnku, wanda kuka yi wa kanku.

  20. Ko da yake kina firiya kamar gaggafa kin kuma yi sheƙarki a can cikin taurari, daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji.

  21. suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”

  22. Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake.

  23. Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.

  24. Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira.

  25. Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja.