Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Stars

57 ayoyi · 40 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru,

  2. Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari.

  3. Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya,

  4. Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”

  5. “Na gan shi, amma ba yanzu ba; na hange shi, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga Yaƙub; sandan mulki zai fito daga Isra’ila. Zai ragargaje goshin Mowab, kawunan dukan ’ya’yan Set.

  6. Sa’ad da kuka ɗaga ido kuka kali sama, kuka ga rana da wata, da taurari, da dukan halittun sama, sai ku kula fa, kada ku jarrabtu, ku ce za ku yi musu sujada, ko ku bauta musu; abubuwan nan Ubangiji Allahnku ne ya rarraba wa dukan al’umman da suke ko’ina a ƙarƙashin sararin sama.

  7. In an sami wani namiji ko ta mace mai zama a cikinku, a ɗaya daga biranen da Ubangiji ya ba ku yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku ta wurin karya alkawarinsa,

  8. wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama,

  9. in kuwa aka faɗa muku wannan, to, dole a bincika sosai. In kuwa gaskiya ne, aka kuma tabbatar cewa wannan abin ƙyama ya faru a cikin Isra’ila,

  10. sai a ɗauki namijin, ko ta mace wanda ya aikata wannan mugun abu zuwa ƙofar birni, a jajjefe wannan mutum sai ya mutu.

  11. Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku, za a iya kashe mutum, amma ba za a iya kashe mutum bisa ga shaida mutum guda ba.

  12. Hannuwan shaidun ne za su zama na farko a kisan wanda ake zargin, sa’an nan hannuwan dukan mutane. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  13. Daga sama taurari suka yi faɗa, daga bakin tekuna suka yi yaƙi da Sisera.

  14. Ya kawar da firistocin gumakan da sarakunan Yahuda suka naɗa don su ƙona turare a masujadan kan tuddai na garuruwan Yahuda, da kuma waɗanda suke kewaye da Urushalima, masu ƙona turare wa Ba’al, rana da wata, ga rukunin taurari, da kuma ga dukan rundunan taurari.

  15. Saboda haka muka ci gaba da aiki, rabin mutane suna riƙe da māsu, daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari.

  16. Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani,

  17. Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske.

  18. Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.

  19. In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa,

  20. yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.

  21. “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?

  22. Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?

  23. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,

  24. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  25. Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.