Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Power of Christ

62 ayoyi · 34 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.

  2. Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama.

  3. Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.

  4. Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa.

  5. “Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa

  6. su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.

  7. Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”

  8. Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

  9. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.

  10. Da ni da Uba ɗaya ne.”

  11. “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  12. Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.

  13. Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.

  14. yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.

  15. Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku.

  16. Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko.

  17. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

  18. da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya.

  19. Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.

  20. Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya.

  21. shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

  22. Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  23. Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne.

  24. Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.

  25. Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.