Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Power of Christ: As the Son of God, is the power of God
Ayoyi game da As the Son of God, is the power of God
Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.”
Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.
Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.
Da ni da Uba ɗaya ne.”