Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus

607 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta.

  2. Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”

  3. Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.”

  4. Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”

  5. Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

  6. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,

  7. sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami.

  8. Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi.

  9. Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai,

  10. waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.”

  11. Ba haka ya kamata yă zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yă zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku.

  12. Duk wanda kuma yake so yă zama na farko, dole yă zama bawan kowa.

  13. Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

  14. Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”

  15. “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!”

  16. Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.

  17. Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne.

  18. Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.

  19. Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya.

  20. Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu.

  21. Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi.

  22. Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi.

  23. Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.

  24. “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’

  25. “Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’