Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus

607 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi.

  2. Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba,

  3. ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”

  4. Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada,

  5. inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.

  6. Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.”

  7. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’”

  8. Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya.

  9. Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama.

  10. Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”

  11. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”

  12. Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.

  13. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau;

  14. za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”

  15. Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”

  16. Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.

  17. “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

  18. In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”

  19. Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

  20. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.

  21. Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”

  22. “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa?

  23. Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata.

  24. Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.

  25. Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”