Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Christ Jesus

607 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)

  2. Yesu ya ci gaba da cewa, “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke?

  3. Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, “ ‘Mun busa muku sarewa, amma ba ku yi rawa ba, Mun kuma yi muku waƙar makoki, ba ku kuma yi kuka ba.’

  4. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’

  5. Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’

  6. Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta.”

  7. Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma

  8. Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi.

  9. Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”

  10. “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.

  11. “Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’

  12. Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye.

  13. Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”

  14. “Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta ƙunu!

  15. Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta!

  16. Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne.

  17. Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun.

  18. Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”

  19. Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina.

  20. Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’

  21. Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa.

  22. Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’

  23. “Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’

  24. “Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’

  25. “Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’