Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The, Are Compared To Wicked

58 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama asu za su cinye su kamar riga; tsutsotsi za su cinye su kamar ulu. Amma adalcina zai dawwama har abada, cetona har dukan zamanai.”

  2. A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro, a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro. Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi, madawwamiyar alama ce, wadda ba za a datse ba.”

  3. Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, wanda ba ya natsuwa, wanda raƙumansa sukan kawo gurɓacewa da tabo.

  4. Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne.

  5. Ana ce da su azurfar da aka ƙi, gama Ubangiji ya ƙi su.”

  6. Na saurara sosai, amma ba su faɗi wata maganar kirki ba. Ba wanda ya tuba daga muguntarsa, sai ma cewa yake, “Me na yi?” Kowa ta kai-ta-kai yake kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama.

  7. Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango; ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba. Za su zauna a busassun wuraren hamada, a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

  8. “ ‘Amma kamar ’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar.

  9. Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye.

  10. “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai.

  11. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku duka kun zama ƙwan maƙera, zan tattara ku a Urushalima.

  12. Dukansu mazinata ne suna ƙuna kamar matoya wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta daga cuɗe kullu har kumburinsa.

  13. Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga.

  14. “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa.

  15. “Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  16. Sa’an nan za ku tattake mugaye; za su zama toka a ƙarƙashin tafin ƙafafunku a ranar da zan aikata waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  17. Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

  18. “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.

  19. Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.

  20. “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

  21. Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi.

  22. Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan,

  23. Da abin kamun kifi ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau.

  24. Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne.In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”

  25. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta.