Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Spear

41 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi

  2. Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka riƙe māshin da yake hannunka ka nuna wajen Ai, gama zan ba da birnin a hannunka.” Yoshuwa kuwa ya miƙa māshin ta wajen Ai.

  3. Sa’ad da suka zaɓi sababbin alloli, sai ga yaƙi a ƙofofin birnin, ba a kuwa ga garkuwa ko māshi a cikin mutum dubu arba’in a Isra’ila ba.

  4. Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.”

  5. A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko māshi ba a cikin mutanen da suke tare da Shawulu da Yonatan. Sai dai Shawulu da ɗansa Yonatan kaɗai.

  6. Ƙotar kibiyarsa kuwa kamar sandar saƙar igiya take, ƙarfen kibiyar kuma nauyinsa ya kai shekel ɗari shida. Mai riƙe masa garkuwa yana tafe a gabansa.

  7. Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.

  8. Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu.

  9. Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.

  10. Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.

  11. Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”

  12. Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira?

  13. Muddin Ubangiji yana a raye, Ubangiji da kansa zai buge shi, ko yă mutu a lokacinsa, ko kuma yă mutu a wurin yaƙi.

  14. Amma Allah yă sawwaƙa in sa hannu a shafaffen Ubangiji, ka ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da kansa mu tafi.”

  15. Amma Asahel ya ƙi yă bar fafararsa; saboda haka Abner ya soki Asahel da māshinsa a ciki; har māshin ya fita ta bayansa. Nan take ya fāɗi, ya mutu. Kowa da ya zo wurin da Asahel ya fāɗi, ya mutu, sai yă tsaya.

  16. Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci da kai ba.” Saboda haka sai ya ɗauki māsu uku a hannunsa ya zura su a ƙahon zuciyar Absalom, tun Absalom yana da sauran rai a maƙale a itacen oak.

  17. Ishbi-Benob kuwa, wani daga zuriyar Rafa, wanda nauyin kan māshinsa na tagulla ya yi shekel ɗari uku, wanda yake kuma da sabon māshi, ya ce zai kashe Dawuda.

  18. Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.

  19. Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.

  20. Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.

  21. Sa’an nan ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin haikalin Allah.

  22. Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.

  23. Saboda haka na sa jama’a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan katanga, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakkuna.

  24. Daga wannan rana zuwa gaba, rabin mutane suka yi aiki, yayinda sauran rabin suka kintsa da māsu, da garkuwa, da bakkuna da makamai. Shugabanni suka goyi bayan dukan mutanen Yahuda

  25. Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.