Skip to content

Millo

6 verses

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Millo

  1. Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki.

  2. Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer.

  3. Bayan ’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini.

  4. Ga yadda ya tayar wa sarki Solomon. Sarki Solomon ya gina madogaran gini, ya ciccika wurare a katangar birnin Dawuda mahaifinsa da ƙasa.

  5. Sai ya gina birni kewaye da shi, daga madogaran gini zuwa katangar da take kewaye, yayinda Yowab ya maido da sauran birnin.

  6. Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.