Tsallake zuwa abun ciki

Daughter of Pharaoh

5 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Daughter of Pharaoh

  1. Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.

  2. A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro.

  3. Bayan ’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini.

  4. Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa.

  5. Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”