Skip to content

Pharaoh

9 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Pharaoh

  1. Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.

  2. (Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga ’yarsa, matar Solomon.

  3. Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa.

  4. Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci.

  5. Fir’auna ya ji daɗin Hadad har ya ba shi ’yar’uwar matarsa, Sarauniya Tafenes, aure.

  6. ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da ’ya’yan Fir’auna.

  7. Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.”

  8. Fir’auna ya tambaye shi, ya ce, “Me ka rasa a nan da kake so ka koma garinka?” Ya ce, “Ba kome, amma ka dai bar ni in tafi!”

  9. Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”