Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”

  2. Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?

  3. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

  4. Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.

  5. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu.

  6. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.

  7. Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

  8. Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.

  9. Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela

  10. Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.

  11. Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.

  12. Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.

  13. Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.

  14. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.

  15. Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  16. Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?

  17. Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. Sela

  18. Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.

  19. Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  20. Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.

  21. Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Sela

  22. Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.

  23. Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.

  24. Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,

  25. kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”