- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi.
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela
Ta Dawuda. Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba.
Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina;
gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya;
na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.
Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.
Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune.
Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai
waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.
Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.
Ta Dawuda. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro?
Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi.
Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa.
Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.
Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.
Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji; ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini.
Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!” Fuskarka, Ubangiji, zan nema.
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni, kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi; kai ne ka kasance mai taimakona. Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni, Ya Allah Mai cetona.