Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni, Ubangiji zai karɓe ni.

  2. Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji; ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya saboda masu danne ni.

  3. Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina, gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina, suna numfasa tashin hankali.

  4. Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai.

  5. Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.

  6. Ta Dawuda. A gare ka nake kira, ya Ubangiji Dutsena; kada ka yi mini kunnen ƙashi. Gama in ka yi shiru, zan zama kamar waɗanda suka gangara rami.

  7. Ka ji kukata ta neman jinƙai yayinda nake kira ka don neman taimako, yayinda nake daga hannuwana wajen Wurinka Mafi Tsarki.

  8. Kada ka ja ni tare da mugaye, tare da masu yin mugunta, masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu amma suna riƙe da su a zukatansu.

  9. Ka sāka musu da ayyukansu da kuma don mugun aikinsu; ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi ka kuma mayar musu abin da ya dace da su.

  10. Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji da abin da hannuwansa suka yi ba, zai rushe su ba kuwa zai ƙara gina su ba.

  11. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya ji kukata na neman jinƙai.

  12. Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

  13. Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa, kagarar ceto domin shafaffensa.

  14. Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka; ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada.

  15. Zabura ta Dawuda. Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

  16. Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

  17. Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.

  18. Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take.

  19. Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.

  20. Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji.

  21. Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya.

  22. Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.

  23. Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”

  24. Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.

  25. Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.