Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.

  2. Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.

  3. Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai.

  4. Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

  5. Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

  6. Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.

  7. Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske.

  8. Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.

  9. Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni.

  10. Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!

  11. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda. Na ce, “Zan lura da hanyoyina zan kuma kiyaye harshena daga zunubi; zan sa linzami a bakina muddin mugaye suna a gabana.”

  12. Na yi shiru, ban ce kome ba, Ko a kan abin da yake da kyau! Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi;

  13. zuciyata ta ƙara zafi a cikina. Kuma sa’ad da nake tunani, wuta ta yi ta kuna; sai na yi magana da harshena na ce,

  14. “Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata da kuma yawan kwanakina; bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.

  15. Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela

  16. “Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa. Yana ta yawo, amma a banza ne kawai; yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.

  17. “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema? Begena yana a gare ka.

  18. Ka cece ni daga dukan laifofina; kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.

  19. Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba, gama kai ne wanda ka aikata wannan.

  20. Ka ɗauke bulalarka daga gare ni; na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini.

  21. Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela

  22. “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.

  23. Ka kau da fuskarka daga gare ni, saboda in sāke yin farin ciki kafin in tafi in kuma rabu da nan.”

  24. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.

  25. Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.