Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pride

303 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,

  2. na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.

  3. Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’

  4. Saboda haka, mutane suke girmama shi, ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?”

  5. Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela

  6. Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi, waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya.

  7. Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji.

  8. Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah.

  9. Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni.

  10. Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.”

  11. Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.”

  12. Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,

  13. masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”

  14. Kakan cece mai sauƙinkai amma kakan ƙasƙantar da masu girman kai.

  15. Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa! Ubangiji yakan adana amintattu, amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke.

  16. Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.

  17. Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.

  18. “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”

  19. Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.

  20. Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya.

  21. Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya.

  22. Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.

  23. Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”

  24. Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

  25. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.