Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parents: Involved in children's wickedness

23 ayoyi · 48 fannoni

Ayoyi game da Involved in children's wickedness

  1. Wani mutum ya zo wurin Eli ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ashe ban bayana kaina sosai ga mahaifinka lokacin da yake a Masar a ƙarƙashin Fir’auna ba?

  2. Na zaɓi mahaifinka daga cikin dukan kabilar Isra’ila yă zama firist nawa don yă yi hidima a bagade, don yă ƙona turare mai ƙanshi, don kuma yă sanya doguwar riga a gabana. Na kuma ba wa iyalin mahaifinka dukan hadaya ta ƙonawa da Isra’ila suka miƙa.

  3. Don me kuke rena hadayata da sadakokina da na ƙayyade domin mazaunina? Don me kake girmama ’ya’yanka fiye da ni ta wurin cinye sashe mafi kyau na kowane hadayar da mutanena Isra’ila suka miƙa?’

  4. “Saboda haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na yi alkawari cewa gidanka da gidan mahaifinka za su yi mini hidima a gabana har abada.’ Amma, yanzu Allah ya ce, ba zai yiwu ba; waɗanda suke girmama ni; Ni ma zan girmama su. Amma waɗanda suke ƙasƙantar da ni, haka za a ƙasƙantar da su.

  5. Lokaci yana zuwa sa’ad da zan rage ƙarfinka da ƙarfin iyalin gidan mahaifinka. Domin kada a sāke samun tsohon mutum a zuriyarka.

  6. Za ka zama da ɓacin rai a mazaunina ko da yake za a yi wa Isra’ila alheri. A zuriyarka ba za a taɓa samun tsohon mutum ba.

  7. Kowannenku da ban kashe daga hidima a bagadena ba, za a bar shi don yă cika idanunka da hawaye da kuma baƙin ciki, dukan sauran zuriyarka kuwa za su mutu a ƙuruciyarsu.

  8. “ ‘Abin da kuma ya faru da ’ya’yanka biyu Hofni da Finehas zai zama alama a gare ka; saboda mutuwarsu za tă zama a rana ɗaya.

  9. Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so yă yi, zan kuwa ba shi zuriya da koyaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.

  10. Sa’an nan duk wanda ya rage a zuriyarka zai zo yă durƙusa a gabansa yă roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa yă taimaki firistoci da aiki domin yă sami abin da zai ci.’ ”

  11. Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin.

  12. Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.

  13. A wannan rana wani mutumin Benyamin ya ruga da bakin dāgā ya shigo Shilo, taguwarsa a yage, kansa kuma a rufe da ƙasa.

  14. Da ya iso sai ga Eli zaune a kujera kusa da hanya yana kallo, domin tsoron da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shigo a garin ya ba da labarin abin da ya faru sai dukan gari ya ruɗe da ihu.

  15. Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu? Mutumin ya rugo wurin Eli,

  16. wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.

  17. Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.” Eli ya ce, “Me ya faru da ’ya’yana?”

  18. Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

  19. Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.

  20. Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta.

  21. Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.

  22. Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta.

  23. Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”