Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parents

156 ayoyi · 48 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai.

  2. Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi,

  3. sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.”

  4. Ibrahim ya kuma ce wa Allah, “Me zai hana a dai bar Ishmayel kawai yă gāji alkawarin nan da ka yi mini.”

  5. Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”

  6. Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya.

  7. Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata.

  8. Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba.

  9. Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.”

  10. Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana.

  11. Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka.

  12. Sa’an nan Isuwa ya ɗaga ido ya ga mata da ’ya’ya. Ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan tare da kai?” Yaƙub ya amsa, “Su ne ’ya’yan da Allah cikin alheri ya ba bawanka.”

  13. Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’

  14. “Saboda haka yanzu, in saurayin ba ya nan tare da mu sa’ad da na koma ga bawanka mahaifina, in kuma mahaifina, wanda ransa yana daure kurkusa da ran saurayin,

  15. Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi.

  16. Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.

  17. Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,

  18. Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.”

  19. Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse.

  20. Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”

  21. Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.”

  22. Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.

  23. “Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko.

  24. Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.

  25. “Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali.