Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parents: Paternal reproaches

7 ayoyi · 48 fannoni

Ayoyi game da Paternal reproaches

  1. Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi,

  2. sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.”

  3. “Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko.

  4. Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.

  5. “Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali.

  6. Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai.

  7. La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.