Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nineveh

49 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala

  2. da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.

  3. Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.

  4. Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.

  5. Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can.

  6. Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok, ’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.

  7. Maganar Ubangiji ta zo wa Yunana ɗan Amittai cewa,

  8. “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.”

  9. Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu.

  10. “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”

  11. Sai Yunana ya yi biyayya da maganar Ubangiji, ya tafi Ninebe. Ninebe birni ne da yake da muhimmanci, wanda sai an ɗauki kwana uku kafin a iya zaga shi.

  12. A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?”

  13. Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.

  14. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.

  15. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha.

  16. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.

  17. Wa ya sani? Ko Allah zai ji tausayinmu da kuma juyayinmu yă janye zafin fushinsa don kada mu hallaka.”

  18. Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.

  19. Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”

  20. amma da ambaliyar ruwa zai kawo Ninebe ga ƙarshe; zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu.

  21. Dukan abin da suke ƙullawa game da Ubangiji zai kawo ga ƙarshe; wahala ba za tă sāke komowa ƙaro na biyu ba.

  22. Za su sarƙafe a ƙaya, za su kuma bugu da ruwan inabinsu; za a laƙume su kamar busasshiyar ciyawa.

  23. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa, za a yanke su, a kawar a su. Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda, ba zan ƙara ba ki azaba ba.

  24. Ubangiji ya ba da umarni game da ke Ninebe, “Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba. Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera gumakan da suke a cikin haikalin allolinku. Zan shirya kabarinki, domin ke muguwa ce.”

  25. Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki!