Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Milk

40 ayoyi · 23 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.

  2. raƙuma mata talatin tare da ƙananansu, shanu arba’in da bijimai goma, jakuna mata ashirin da kuma jakuna maza goma.

  3. Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara.

  4. Saboda haka na sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in kuma fitar da su daga ƙasar Masar, in kai su ƙasa mai kyau mai fāɗi, ƙasa mai zub da madara da zuma, inda Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa suke.

  5. Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’

  6. Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata.

  7. “Dole ne ku kawo mafi kyau daga nunan fari na gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.

  8. Ka haura zuwa ƙasar da take zub da madara da zuma. Amma ba zan tafi tare da ku ba, saboda ku mutane ne masu taurinkai domin mai yiwuwa in hallaka ku a hanya.”

  9. Suka ce wa Musa, “Mun je ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana zub da madara da zuma! Ga kuma amfaninta.

  10. Kada ku ci abin da kun samu ya riga ya mutu. Za ku iya ba wa baren da yake zama a cikin wani daga biranenku, zai kuwa iya cinsa, ko kuwa za ku iya sayar da shi wa baƙo. Amma ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madara mamansa.

  11. Ya kawo mu wannan wuri, ya kuma ba mu wannan ƙasa, ƙasa mai zub da madara da kuma zuma;

  12. Ka duba ƙasa daga sama, mazauninka mai tsarki, ka albarkace mutanenka Isra’ila da kuma ƙasar da ka ba mu kamar yadda ka yi wa kakanninmu alkawari da rantsuwa, ƙasa mai zub da madara da zuma.”

  13. da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa.

  14. Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka.

  15. Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.

  16. Ya nemi ruwa, ta kuwa ta ba shi madara; a ƙwaryar da ta dace da sarakuna ta kawo masa kindirmo.

  17. “Yanzu fa ku shirya sabon keken shanu da shanu biyu masu ba wa ’ya’yansu nono, waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba. Ku daure keken shanu wa shanun, amma ku tsare ’yan maruƙansu a gida.

  18. Suka yi haka. Suka ɗauki shanun tatsa guda biyu suka ɗaura musu keken shanu, suka tsare ’yan maruƙansu a gida.

  19. Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.

  20. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;

  21. Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.

  22. Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.”

  23. Leɓunanki suna zub da zaƙi kamar kakin zuma, amaryata; madara da zuma suna a ƙarƙashin harshenki. Ƙanshin rigunanki ya yi kamar na Lebanon.

  24. Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ƙawaye Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.

  25. A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai.