Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Milk: Used for food

5 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da Used for food

  1. Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.

  2. Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.

  3. Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ƙawaye Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.

  4. saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku.

  5. Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa?