Skip to content

East

6 verses

31.9500, 35.9200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci East

  1. Duk lokacin da Isra’ilawa suka yi shuka sai Midiyawa da Amalekawa da waɗansu mutane daga gabashi sukan kai musu hari.

  2. To, dukan Midiyawa, Amalekawa da sauran mutanen gabashi suka haɗa ƙarfi suka ƙetare Urdun suka kafa sansani a Kwarin Yezireyel.

  3. Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge.

  4. To, Zeba da Zalmunna suna a Karkor da mayaƙa wajen dubu goma sha biyar, abin da ya rage ke nan na mayaƙan gabashi; mayaƙa masu takobi dubu ɗari da ashirin ne suka mutu.

  5. saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku.

  6. Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai;