Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Milk

40 ayoyi · 23 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma.

  2. “Ku zo, dukanku masu jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye; ku kuma da ba ku da kuɗi, ku zo, ku saya ku kuma ci! Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.

  3. Za ki sha madarar al’ummai a kuma shayar da ke da nonon sarauta. Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub.

  4. Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.”

  5. Ka ba su wannan ƙasa da ka rantse za ka ba wa kakanni kakanninsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.

  6. Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.

  7. ’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu.

  8. A ranar na yi musu rantsuwa cewa zan fitar da su daga Masar zuwa ƙasar da na samo musu, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe.

  9. saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku.

  10. “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi, tuddai kuma za su malmalo madara; dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa. Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.

  11. Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba.

  12. Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa?

  13. Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yă sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai kauri ba!

  14. Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar jariri ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba.

  15. Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku,