Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Man

106 ayoyi · 114 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.

  2. Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”

  3. Dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifayen teku, za su riƙa jin tsoronku, suna fargaba. An sa su a cikin hannuwanku.

  4. Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.

  5. In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,

  6. to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!

  7. Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada.

  8. Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’

  9. Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.

  10. Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?

  11. “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?

  12. Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?

  13. Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.

  14. Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?

  15. “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?

  16. Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?

  17. “Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka?

  18. Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba?

  19. Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?

  20. In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa,

  21. mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”

  22. “Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’

  23. Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’

  24. “Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka.

  25. Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku.