Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faith

543 ayoyi · 124 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana.

  2. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

  3. Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”

  4. Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.

  5. Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.

  6. Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,

  7. don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.

  8. Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.

  9. Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

  10. Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.”

  11. In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata,

  12. to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.

  13. Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba.

  14. Za a sāke kafa hukunci a kan adalci, kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.

  15. Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.

  16. Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

  17. Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom?

  18. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

  19. Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.

  20. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu.

  21. Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

  22. Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.

  23. Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu. Zai albarkace gidan Isra’ila, zai albarkace gidan Haruna,

  24. zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji, manya da ƙanana duka.

  25. Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru, da ku da ’ya’yanku.