Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faith: General references

147 ayoyi · 124 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.

  2. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

  3. Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,

  4. don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa.

  5. Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.

  6. Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.

  7. Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare.

  8. Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.

  9. Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

  10. Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.

  11. Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.

  12. Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

  13. Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,

  14. don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.

  15. Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.

  16. Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

  17. Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.

  18. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum.

  19. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna.

  20. “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

  21. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  22. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.

  23. In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”

  24. Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”

  25. Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”