Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faith: Exemplified

240 ayoyi · 124 fannoni

Ayoyi game da Exemplified

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan rera waƙa ga Ubangiji gama an ɗaukaka shi ƙwarai. Doki da mahayinsa ya jefa su cikin teku.

  2. “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata, ya zama cetona. Shi Allahna ne, zan yabe shi. Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.

  3. Ubangiji mai yaƙi ne Ubangiji ne sunansa.

  4. Karusan Fir’auna da sojojinsa ya jefa cikin teku. Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.

  5. Zurfafan ruwaye sun rufe su; suka nutse cikin zurfi kamar dutse.

  6. Hannun damanka, ya Ubangiji, Mai kwarjini ne da iko, hannun damanka, ya Ubangiji, ya farfashe magabci.

  7. “A cikin girman kwarjininka ka kā da waɗanda sun yi gāba da kai. Ka aiki fushinka mai zafi ya cinye su kamar tattaka.

  8. Da hucin numfashin hancinka ruwaye suka tattaru. Ruwaye masu kwararowa, suka tsaya kamar bango; ruwaye na zurfafa suka daskare a tsakiyar teku.

  9. Magabci ya yi fahariya, cewa ‘Zan fafare su, in ci musu. Zan raba ganima; abin da na so ya samu. Zan ja takobina hannuna kuwa zai hallaka su.’

  10. Amma ka hura numfashinka sai teku ya rufe su. Suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.

  11. Wane ne cikin alloli, ya yi kamar ka, ya Ubangiji? Wane ne kamar ka, mai ɗaukaka cikin tsarki, mai banrazana cikin ɗaukaka, mai aikata al’ajabai?

  12. “Ka miƙa hannunka na dama, ƙasa ta haɗiye abokan gābanka.

  13. A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe mutanen da ka fansa. A cikin ƙarfinka, za ka bishe su zuwa mazauninka mai tsarki.

  14. Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki tsoro zai kama mutanen Filistiya.

  15. Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.

  16. Razana da tsoro za su fāɗo a kansu. Da ikon hannunka za su tsaya cik kamar dutse, har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.

  17. Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka inda, ya Ubangiji, ka shirya domin mazauninka, wuri mai tsarkin da hannuwanka suka kafa, ya Ubangiji.

  18. “Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”

  19. Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.

  20. In Ubangiji ya ji daɗinmu, zai kai mu ƙasan nan, ƙasar da take zub da madara da zuma, yă kuwa ba mu ita.

  21. Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji. Kada kuma ku ji tsoron mutane ƙasar, domin za mu gama da su. Kāriyarsu ta gama, amma Ubangiji yana nan tare da mu. Kada ku ji tsoronsu.”

  22. Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.

  23. Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”

  24. Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.

  25. Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.