Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faith

543 ayoyi · 124 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni, ba zan sha kunya ba. Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara, na kuma sani ba zan sha kunya ba.

  2. Gama shi da zai tabbatar da ni, marar laifi ne yana kusa. Wane ne zai kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari’a tare! Wane ne mai zargina? Bari yă kalubalance ni!

  3. Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni. Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi? Duk za su koɗe kamar riga; asu za su cinye su.

  4. “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

  5. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  6. Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.”

  7. Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;

  8. yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.

  9. Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.

  10. Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.

  11. Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.

  12. Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.

  13. Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada.

  14. Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.

  15. A wannan lokaci sai waɗansu masanan taurari suka zo gaba suka yi karar Yahudawa.

  16. Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ran sarki yă daɗe,

  17. Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya,

  18. kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta.

  19. Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”

  20. Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki,

  21. sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa?

  22. Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

  23. Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu.

  24. In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka.

  25. Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.”