Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faith

543 ayoyi · 124 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā.

  2. Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar.

  3. Waɗannan mutanen suna sanye da riguna, da wanduna, da rawani da waɗansu kayan sawa, aka daure su, aka jefa su cikin tanderun wuta.

  4. Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego,

  5. waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar.

  6. Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.”

  7. Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.”

  8. Sai Nebukadnezzar ya matsa kusa da ƙofar tanderun wutar ya yi kira da ƙarfi, “Shedrak, Meshak da Abednego, bayin Allah Mafi Ɗaukaka ku fito! Ku zo nan!” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka fita daga cikin wutar,

  9. Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba.

  10. Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu.

  11. Domin haka ina ba da doka cewa duk mutane da kowace al’umma ko kowane yaren da ya ce wani abu mummuna a kan Allahn Shadrak, Meshak da Abednego za a yanka shi gunduwa-gunduwa kuma gidansu zai zama wurin zuba shara, domin babu wani allahn da zai iya ceto ta irin wannan hanya.”

  12. Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon.

  13. Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata.

  14. Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina.

  15. Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’

  16. Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni.

  17. Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna.

  18. “Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki.

  19. “Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani, sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu.

  20. Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”

  21. Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji, ina sauraron Allah Mai Cetona; Allahna kuwa zai ji ni.

  22. Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana! Ko da yake na fāɗi, zan tashi. Ko da yake na zauna a cikin duhu, Ubangiji zai zama haskena.

  23. Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da ’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa.

  24. Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba.

  25. “Duba, abokin gāba ya cika da ɗaga kai; sha’awarsa ba daidai ba ce, amma mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiyarsa,