Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faith

543 ayoyi · 124 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa.

  2. Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu.

  3. A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.

  4. Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji, ko ma da muke sa begenmu a gare ka.

  5. Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.

  6. Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.

  7. Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare.

  8. Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.

  9. Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

  10. Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.

  11. Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.

  12. Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

  13. Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala.

  14. Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi.

  15. Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.

  16. Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.

  17. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.

  18. Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.

  19. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

  20. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

  21. ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

  22. Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.

  23. Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela

  24. Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni.

  25. Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.