Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Faith

543 ayoyi · 124 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

  2. Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

  3. Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

  4. Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.

  5. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.

  6. Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka, ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.

  7. Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.

  8. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,

  9. Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.

  10. Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?

  11. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?

  12. Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.

  13. Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.

  14. Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.

  15. Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  16. Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.

  17. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.

  18. Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.

  19. gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,

  20. ’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.

  21. Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro.

  22. Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka.

  23. Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi.

  24. Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni.

  25. Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni.