Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children

257 ayoyi · 102 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya ce musu, “Yayinda yaron yake da rai, na yi azumi, na kuma yi kuka. Na yi tunani na ce, ‘Wa ya sani? Ko Ubangiji zai yi mini alheri yă bar yaron yă rayu.’

  2. Amma yanzu da ya mutu, me zai sa in yi azumi? Zan iya dawo da shi ne? Ni zan je wajensa, ba shi zai dawo wurina ba.”

  3. Saboda haka a rana ta farko ga watan bakwai, Ezra firist, ya kawo Doka a gaban taro, wanda ya ƙunshi maza da mata da dukan waɗanda za su iya fahimta.

  4. Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar.

  5. sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan ’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”

  6. Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada

  7. ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.”

  8. Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala; kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu,

  9. kana kāre marayu da waɗanda aka danne, domin mutum, wanda yake na duniya kada ƙara haddasa wata razana.

  10. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,

  11. tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

  12. ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.

  13. Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada.

  14. ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi.

  15. Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

  16. Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  17. Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

  18. Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.

  19. Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.

  20. Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.

  21. Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.

  22. Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.

  23. ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba.

  24. A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu.

  25. Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa, rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa; zan ba da Ruhuna ga ’ya’yanka, albarkata kuma ga zuriyarka.