Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children: Inherited property in default of sons

14 ayoyi · 102 fannoni

Ayoyi game da Inherited property in default of sons

  1. ’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.

  2. Da suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada, sai suka tsaya a gaban Musa, Eleyazar firist, shugabannin da sauran taro, suka ce,

  3. “Mahaifinmu ya mutu a hamada. Ba ya cikin mabiyan Kora waɗanda suka taru suka tayar wa Ubangiji, amma ya mutu ne saboda zunubinsa, bai kuma bar ’ya’ya maza ba.

  4. Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.”

  5. Saboda haka Musa ya kawo maganarsu a gaban Ubangiji.

  6. Ubangiji kuwa ya ce wa masa,

  7. “Abin da ’ya’yan nan mata na Zelofehad suke faɗi gaskiya ne. Dole ka ba su mallaka a matsayin gādo cikin ’yan’uwan mahaifinsu, ka kuma mayar musu da gādon mahaifinsu.

  8. “Ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘In wani ya mutu ba shi da ɗa, a ba da gādonsa ga ’yarsa.

  9. Wannan shi ne gādon da aka ba wa kabilar Manasse, a matsayin ɗan farin Yusuf. Manasse yana da ɗan farin mai suna Makir. Makir shi ne mahaifin mutanen Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan gama Makiriyawa jarumai ne ƙwarai.

  10. Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manasse rabon gādonsu bisa ga iyalansu, wato, Abiyezer, Helek, Asriyel, Shekem, Hefer da Shemida. Waɗannan su ne ’ya’yan Manasse, maza, ɗan Yusuf bisa ga iyalansu.

  11. Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse ba shi da ’ya’ya maza, sai dai mata. Ga sunayensu, Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.

  12. Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji.

  13. Dalilin ke nan Manasse ya sami kashi goma ban da ƙasar Gileyad da Bashan a gabashin Urdun,

  14. domin ’ya’ya mata na kabilar Manasse sun sami gādo tare da ’ya’ya maza. Aka ba wa sauran mutanen kabilar Manasse ƙasar Gileyad.